Wata mata mai suna Furera Abubakar, ta kashe jaririn da kishiyarta ta haifa mai kwana hudu a kauyen Bantu da ke Karamar Hukumar Ningi a Jihar Bauchi.
Alfijir Labarai ta rawaito Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Ahmed Wakil, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Talata.
Kungiyar Tarayyar Afirka ta dakatar da Nijar daga cikinta
Mahaifi ya daddatsa dansa a kan rogo
Ya ce, “Binciken farko-farko ya nuna cewa wacce ake zargi da kisan, kishiyar wacce aka kashe wa dan ce.
“Wacce ake zargin ta shiga dakin kishiyar tata ne da guba (ta Gamale), inda ta zuba wa jaririn a baki.
“Gubar da aka zuba wa jaririn a baki ta sa ya fara rashin lafiya nan take, wanda daga bisani ya yi sanadiyyar rasuwarsa.”
Wakil ya ce bayan faruwar lamarin, an kai rahoto a ofishinsu da ke Ningi, a ranar 19 ga watan Agusta, kwana hudu bayan haihuwar jaririn.
Ya kuma ce yanzu haka suna ci gaba da bincike, kuma da zarar sun kammala, za su gurfanar da wacce ake zargin a gaban kuliya.
Aminiya
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM