Daga Aminu Bala Madobi
Wasu jiga-jigan ‘yan siyasa uku a Najeriya Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, Rabi’u Kwankwaso na jam’iyyar NNPP da Peter Obi Na LP suka fara shirin kulla kawancen kwace mulki daga Jam’iyyar APC.
Alfijir Labarai ta rawaito idan za a iya tunawa jiga jigan yan siyasar sun kasance ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 inda suka sha kaye a hannun shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC.
Yayin da Atiku da Peter Obi ke ci gaba da shari’ar neman kujerar Tinubu a matsayin shugaban kasa, Kwankwaso ya gana da Tinubu bayan rantsar da shi a Abuja.
A yayin ganawar, an ce Tinubu yayi alwashin yin gwamnatin hadin kan kasa, ya yi alkawarin baiwa kwankwaso minista, amma daga bisani ba ya cikin sunayen ministoci 48 da za a rantsar a yau a Abuja.
A wani rahoto da jaridar Thisday ta buga, an dade ana tattaunawa tsakanin ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, NNPP da Labour Party (LP) ta bayan fage.
Rahotanni sun bayyana cewa an fara tattaunawa tsakanin Atiku da Kwankwaso inda daga baya aka koma ganawar Obi da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP.
Rahoton ya tabbatar da cewa mutanen ukun sun amince da jiran hukuncin kotun, wanda zai zama alkiblar da za ta haifar da tattaunawa ta gaba tsakanin shugabannin jam’iyyar adawa uku. Wannan ya ta’allaka ne akan cewa kashi na biyu zai kasance idan hukuncin kotu.
A halin da ake ciki, wasu majiyoyi masu zaman kansu a taron sun bayyana cewa shugabannin adawar na da kwarin gwiwar cewa kotun za ta yi adalci a hukuncin da ta yanke na tsige shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC.
Hakazalika, majiyar ta bayyana cewa wadannan shugabanin na fatan asake yin zaben, wanda hakan ka iya haifar da hadakar da jam’iyyar APC da kuma shugaba Tinubu.
Majiyar ta kuma tabbatar da cewa idan hukuncin kotun ya baiwa bangaren jam’iyya mai mulki, za su bukaci zabin yin hadaka a zaben shugaban kasa na 2027.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇