Minjibir ya yi alkawarin cewa mambobin kwamitin za su yi iya kokarinsu don ganin sun kammala aikin a kan lokaci.
Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin mutum 22 domin tantance ma’aikata sana da dubu 10 da aka dakatar, wadanda aka dauka aiki a karshen wa’adin gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Sakataren gwamnatin jihar Kano, Dr. Baffa Bichi, ya ce kwamitin zai tabbatar da ko anbi ka’ida wajen daukar ma’aikata.
Kwamitin zai yi aiki bisa jagorancin shugaban hukumar daukar ma’aikata, Alhaji Umar Shehu Minjibir, kuma an baiwa kwamitin wa’adin makonni uku ya kammala aikinsa.
A martanin da ya mayar, Minjibir ya yi alkawarin cewa mambobin kwamitin za su yi iya kokarinsu don ganin sun kammala aikin a kan lokaci.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM