Matasan su 12 sun gurfanar a gaban kotun Majistre dake zaman ta a unguwar Norman’s Land, mai lamba 16, bisa zarginsu da aikata laifukan hada kai da hallaka wani matashi mai suna Yakubu dake Garin Fiddalami a Saya-saya karamar hukumar Albasu a jahar Kano.
Alfijir Labarai ta rawaito tunda fari wata hatsaniya ta hada su, inda ake zargin sun buga masa itace akansa al’amarin da ya yi sanadiyar rasuwarsa.
Lauyar gwamnati Barista Fatima Garba Yakasai ta shaida wa kotun cewa chajin da ake yiwa wadanda ake zargin babban laifi ne, kuma tuhumar ta bada damar a gurfanar da su a gaban babbar kotun jahar, sakamakon rashin hurumi da kotun majistirin ta ke dashi na ci sauraran shari’ar.
Cikin mutanen da ake zargin shida daga cikin matasan sun gudu, inda aka gurfanar da mutane 6, da suka hada da, Jagari Dogo, Yakubu Shu’aibu, Yusuf Abdulmumini, Babangida Datti, Aminu Saleh da kuma Babangida Lamara.
A karshe mai shari’a Hajara Garba Ahmed ta amince da bukatar lauyar gwamnatin, na maida shari’ar zuwa babbar kotun jahar, an kuma dage shari’ar zuwa ranar 21 ga watan Satumba 2023.
Oddity24
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM