Yawan Sharara Masa Mari Ya Sanya Magidanci Neman Kotu Ta Raba Aurensa Da Matarsa

Marin da matata ke yawan sharara min ne ya sa nake son kotu ta raba aurenmu inji wani miji da ya maka matarsa kotu saboda yawan lakada masa duka.

Alfijir Labarai ta rawaito wani dan kasuwa Rafael Chima ya maka matarsa Joy a kotu a yankin Jikwoyi a babban birnin tarayya Abuja, inda ya ce kodayaushe matar na bashi kashi, kuma ba ta girmama iyayensa.

Rafael ya sanar da kotu cewa yana so kotu ta raba aurensu tun da matar ba ta kula da dan da suka haifa.

Sai dai matar duk ta musanta wadannan zarge-zarge, tace kalan sharri ne kawai.

Shi kuma alkalin kotun Dada Oluwaseyi ya shawarci ma’auratan da su je gida su sasanta kansu, idan kuma abin ya gagara ne to sa iya dawowa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *