Gwamnatin jihar Kano ta soke lasisin duk wasu makarantu masu zaman kansu da ke aiki a jihar
Alfijir Labarai ta rawaito Mai bai wa gwamna shawara na musamman kan makarantu masu zaman kansu, Alhaji Baba Abubakar Umar ne, ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin wata ganawa da masu Makarantu masu zaman kansu.
Yace ana bukatar dukkan makarantu masu zaman kansu da su yi sabuwar rajista cikin gaggawa.
Abubakar ya kara da cewa matakin ya jaddada kudirin gwamnati na ganin cewa makarantu masu zaman kansu sun bi ka’idojin da aka gindaya na gudanar da ayyukansu.
“An tunatar da masu makarantu masu zaman kansu alhakin da ya rataya a wuyansu na biyan harajin kaso 10 ga gwamnati. Wannan kuɗi ko yaushe yana ƙara ci gaba a fannin,” in ji shi.
Mashawarci na musamman ya tabbatar wa duk masu ruwa da tsaki cewa zai tabbatar da adalci wajen kula da ayyukan makarantu masu zaman kansu.
Ya jaddada bukatar aiwatar da ka’idojin aiki ga masu mallakar makarantu masu zaman kansu wadanda suka hada da kayan aiki, yanayin koyo, manhaja da jadawalin koyarwa.
Ya kuma tabbatar wa iyaye fifikon da aka ba su wajen kiyaye muradunsu da na ‘ya’yansu.
Da yake mayar da martani, shugaban kungiyar masu makarantu masu zaman kansu a jihar, Alhaji Muhammad Malam Adamu, ya yaba da matakin da gwamnati ta dauka, yana mai kallon matakin a matsayin abin yabawa a fannin ilimi a jihar.
Adamu ya bayyana muhimmancin yanayin tsarin aiki, yana mai tabbatar da cewa duk wani aiki da ba a bin ka’ida yana samun koma baya.
Ya yi kira ga masu makarantu masu zaman kansu da su hada kai da gwamnati wajen gudanar da sauye-sauyen.
A yayin taron an fitar da wata sabuwar manhaja domin tattara bayanan masu makarantu masu zaman kansu a fadin Kano.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM
Ilimi ginshikin Rawuya, Allah yasa kuma a tabo wajen Hauhawar farashi da ilimin yake fama dashi
Wannan gaskiyane Koda baayi mana free education ba adubi kudaden registration