Daga Aminu Bala Madobi
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya koka, inda ya ce barayin da ba a san su ba sun fara shiga harabar majalisar dokokin kasa domin sace wa Sanatoci wayoyi da sauran kayayyaki masu daraja.
Alfijir Labarai ta rawaito Akpabio ya bayyana hakan ne a lokacin da ‘yan majalisar suka kai masa ziyarar ban girma a harabar najalisar, da ke Abuja.
Ya ce, “Muna sane da cewa ana gyara ginin gaba dayansa, Dole ne mu kuma kula da muhalli.
Ba wai kawai game da ma’aikata ba ne, za mu so mu ga yanayi mai kyau da tsabta.
“Sanatoci da yawa sun rasa wayoyinsu saboda kwararowar mutane cikin rukunin harabar majalisar.”
Shugaban majalisar dattawan ya jaddada cewa an yi wa ‘yan majalisar barazana saboda kasancewar kutse da ake samu na marasa daraja.
A cewar Akpabio, yayin da majalisa ta 10 ke zaman ayyukan ta, ’yan dagaji da mutanen da ba su da wata sana’a a harabar, suka yi kaca-kaca a ko’ina a majalisar dattawa da na wakilai, tare da haifar da rashin tsaro ga ‘yan majalisa da ma’aikatan majalisar dokokin kasar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb
Allah ya kyauta
Allah ya kyauta, ana maganar tsananin da yan kasa suke ciki, suna maganar an sace wayoyin su.