Rundunar ƴan sandan jihar Anambra ta tabbatar da sakin wani shahararren bokan nan mai suna Chukwudozie Nwangwu wanda aka fi sani da “Akwa Okuko Tiwaraki” daga hannun masu garkuwa da mutane.
Alfijir Labarai ta rawaito Kakakin rundunar, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da sakin Nwangwu a yau Asabar.
Ikenga, mataimakin Sufeton Ƴansanda, ya lura cewa masu garkuwa da mutanen sun sako fitaccen bokan da sanyin safiyar yau Asabar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya bayar da rahoton cewa, an yi garkuwa da bokan ne da misalin karfe 11:30 na dare a ranar Lahadi 23 ga watan Yuli a Oba da ke Karamar Hukumar Idemili ta Arewa a Anambra.
A cewar Ikenga, masu garkuwa da mutanen sun tuntubi abokai da ‘yan’uwa kuma sun nemi a basu naira miliyan 300 kuɗin fansa.
“Ina kuma da bayanin cewa ba su biya ba. Ina kuma da labarin wadanda suka yi garkuwa da shi sun sake shi kuma muna kokarin samun bayanai kan abin da ya faru,” inji shi.
Daily Nigerian
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb