Ibtila’i! Wata Sabuwar Amarya Ta Yankewa Angonta Mazakuta (Al Aurarsa)

Rundunar ƴansanda a jihar Katsina, ta tabbatar da cafke wata amarya mai suna Tinene Isa, bisa zargin yanke mazakutar angonta.

Alfijir Labarai ta rawaito Jami’in hulda da jama’a na rundunar Ƴan Sandan ASP Abubakar Aliyu ne ya tabbatar da kamen a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa a yau Laraba a Katsina.

Ya ce lamarin ya faru ne a karamar hukumar Kafur.

Aliyu, wanda bai bayyana sunan wanda ibtila’in ya afku a kansa ba, ya ce yana cikin mawuyacin hali inda ake kula da lafiyarsa a babban asibitin Malumfashi.

Ya ce wacce ake zargin ta yi amfani da reza wajen aikata laifin.

“Na gaya muku, muna gudanar da bincike kan lamarin.

“Amarya ce, ta haura shekara 30, watakila ta dauki lokaci mai tsawo kafin ta yi aure, ko kuma ba aurenta ne na fari ba.

“Ba ni da cikakken bayani, za mu gano duk wadannan a bincikenmu,” in ji shi.

Ya ce za a gurfanar da wacce ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *