Gwamnan Kano Ya Ayyana Hutun Sabuwar Shekarar Musulunci Ta 1445

Sarkin Musulmi, kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ayyana Larabar a matsayin ranar daya ga watan Almuharram na sabuwar shekarar, bayan hijirar Annabi Muhammad (S.A.W).

Alfijir Labarai ta rawaito kwamishinan Yada Labarai na Jihar kano, Baba Halilu Dantiye, ne ya fadi haka a cikin wata sanarwa yau  Talata, a madadin Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf.

Gwamna Abba ya taya Musulmai a fadin duniya murnar sabuwar shekarar, inda ya bukace su da su ci gaba da yi wa kasa da  jihar addu’ar samun ci gaba da habakar tattalin arziki.

“Gwamnan ya kuma roki mutane da su yi amfani da kyawawan halayen addinin Musulunci na tausayi, kaunar juna da kuma kawaici, kamar yadda Annabi Muhammad (S.A.W) ya koyar,” in ji sanarwar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *