Ba Duk Bodojin Kasar Ne Bude Ba, Inji Shugaban Kwastam A Nijeriya

Ba dukkan iyakokin kasar da gwamnatin tarayya ta rufe a fadin Najeriya a shekarar 2018 ba ne aka sake budewa.

Alfijir Labarai ta rawaito Mukaddashin Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam ta Najeriya, Wale Adeniyi, ya ce, manyan kan iyakokin kasa shida ne kawai aka bude a shekarar 2021.

Adeniyi ya bayyana haka ne a ranar Talata bayan wata ganawar sirri da shugaban kasa Bola Tinubu a Aso Villa dake Abuja.

Shugaban Kwastam ya shaidawa manema labarai na fadar gwamnatin jihar cewa, ana ci gaba da gudanar da bitar lamarin da kuma kokarin ganin an cimma tsaron kan iyaka da hadin kan yankin.

Ya ce, duk da haka, za a bayyana sake bude iyakokin.

Adeniyi ya koka da kalubalen fasakwaurin man fetur a kan iyakokin kasar, yana mai cewa cire tallafin man fetur da kuma karin farashin man fetur din zai sa masu fasa-kwaurin man fetur su karye cikin dogon lokaci.

Ya ce da sabbin tsare-tsare na gwamnati, kalubalen da ake fama da shi na safarar muhimman kayayyaki zai ragu.

A cewar shugaban Kwastam din, tattaunawar tasa da shugaban kasar ta ta’allaka ne kan inganta tashoshin jiragen ruwa masu dacewa da masu amfani da su, da fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje da kuma tabbatar da share hajoji na sa’o’i 48 a kusa da tashoshin jiragen ruwa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *