Gwamnatin kano ta cafke tsohon kwamishinan ayyuka na gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, Engr Idris Wada Saleh, da karin wasu mutane biyar.
Alfijir Labarai ta rawaito hukumar karbar Korafe-korafen al’umma ta jihar Kano ta tabbatar da kama kwamishina da wasu mukarraban ma’aikatar sa
Hukumar ta bayyana kama mutanen ne bisa zargin su da wawushe Kudaden Al’umma har Naira Biliyan guda da sunan ayyukan tituna 30 da magudanan ruwa a jihar, da aka bai wasu kamfanoni guda uku North Stone Construction Company Nigeria Limited da Arfat Multiresources Limited da kuma 1st Step Construction Limited.
Cikakken bayani na nan tafe…
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
