Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta shiyyar ta biyu, wadda ta kunshi Legas da Ogun, ta ce jami’anta sun kama wasu mutane biyu da ake zargin sun kware wajen yin kutse a asusun kwastomomin bankin.
Alfijir Labarai ta rawaito kamfanin dillancin labarai na kasa ya ce Hauwa Idris-Adamu, mai magana da yawun rundunar, ta tabbatar da kamen a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata a Legas.
Idris-Adamu ya ce rundunar ta yi aiki ne a kan takardar koke daga bankin United Bank for Africa (UBA) a watan Mayu.
Kakakin ya ce an gano wadanda ake zargin ne a Ijebu Ode, jihar Ogun.
“A ranar 8 ga Mayu, 2023, bankin United Bank for Africa (UBA) ya gabatar da koke ga AIG cewa akwai wasu kungiyoyin da suka kware wajen zamba ta intanet na bankuna daban-daban a Najeriya, musamman ma United Bank for Africa (UBA).”
“Suna yin kutse cikin asusun abokan ciniki kuma suna kwashe musu Kuɗaɗen su.
“Bisa takardar koke, AIG ya umarci tawagar jami’an tsaro daga sashin sa ido na shiyyar, wadanda suka fara aiki tare da taimakon fasahar zamani.
“An gano mutanen biyu ne a maboyar su da ke Ijebu Ode, jihar Ogun.
“Sun yi ikirari da cewa suna da kungiyoyi da yawa a duk fadin Najeriya kuma sun yi amfani da manhaja wajen yin kutse cikin asusun abokan huldar su tare da fitar da kudadensu ba tare da an gano su daga banki ba.
“Tsarin ’yan damfara shine samun lambar wayar abokin ciniki mai alaƙa da BVN don aika kuɗi cikin sauƙi.
“Saboda haka, sama da asusun kwastomomi 1,000 aka sace, kuma an damfari abokan cinikin a fadin kasar,” in ji ta.
Idris-Adamu ya ce binciken da aka yi a kan lamarin ya nuna cewa mambobin kungiyar sun fito ne daga sassa daban-daban na kasar.
Ta kara da cewa ana ci gaba da kokarin cafke duk wadanda ke da alaka da wannan aika-aika.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ