Alfijir Labarai ta rawaito Kotu ta sanya ranar 13 ga watan Yuli domin yanke hukunci kan karar da Godwin Emefiele, dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya CBN ya shigar.
A ranar 9 ga watan Yuni, shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele tare da rokonsa da ya mika aikinsa ga Folashodun Adebisi Shonubi, mataimakin daraktan ayyuka. Washegari, Hukumar DSS ta sanar da cewa Emefiele na hannun ta saboda wasu dalilai na bincike.
Ta bakin lauyansa Joseph Daudu, Emefiele ya shigar da karar hukumar DSS da kuma babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) yana neman a bi masa hakkinsa.
A ranar Juma’a, Hamza Muazu, alkalin kotun, ya umarci wadanda ake kara da su gaggauta ba Emefiele damar ganawa da lauyoyinsa da iyalansa.
A zaman kotun da aka yi a ranar Talata, Tijjani Ghazali, lauya ga AGF, ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara na farko yana kalubalantar hurumin kotun na sauraron karar da mai shigar da kara ya gabatar a gabanta.
Ya ce kama Emefiele tsare shi da hukumar DSS ta yi wani mataki ne na gudanarwa na bangaren zartarwa.
Hukumar ta DSS na kuma kalubalantar hurumin kotun na sauraren karar, inda ta dage cewa akwai umarnin kotun majistare na tsare Emefiele.
Wadanda ake kara sun roki kotun da ta yi watsi da bukatar.

A nasa jawabin, Daudu ya jaddada cewa kotu ce ke da hurumin sauraren lamarin.
A cewarsa, laifukan da aka lissafa a kan wanda yake karewa laifukan gwamnati ne da babbar kotun babban birnin tarayya Abuja.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ