Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu Ya Dakatar Da Gwamnan CBN, Emefiele

Alfijr ta rawaito cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin kasa, Mista Godwin Emefiele, daga aiki ba tare da bata lokaci ba,” in ji daraktan yada labarai, ofishin sakataren gwamnatin tarayya Willie Bassey a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Wannan na zuwa ne bayan binciken da ofishin sa ke yi kuma sauye-sauyen da ake shirin yi a bangaren hada-hadar kudi na tattalin arzikin kasar.

“An umurci Mista Emefiele da ya gaggauta mika al’amuran ofishinsa ga Mataimakin Gwamna mai kulada Sashin Ayyuka, wanda zai yi aiki a matsayin Gwamnan Babban Bankin kasar har zuwa lokacin kammala binciken.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu aFacebook. Alfijr Labarai YouTube. Best Seller ChannelTwitter. @MusabestsellerInstagram. @musa_bestsellerKo a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *