An Bukaci Gwamnatin Kano Ta Biya Biliyan 10 A Gaban Kuliya Kan Rusau

Alfijr ta rawaito wani kamfanin gine gine mai suna Lamash Properties Limited ya sha alwashin kalubalantar rushe Daula otal da gwamnatin jihar Kano ta yi inda ta bukaci da abiya sa Naira Bilyan 10.

Rahotanni sun nuna cewa da sanyin safiyar Lahadi ne gwamnatin jihar Kano ta ruguza wani otel na biliyoyin naira a otal din Daula, bisa zargin saye da sayarwa ba bisa ka’ida ba.

LAMASH Properties Limited, kamfani ne dake gudanar da gine gine da gwamnatin jihar Kano ta gayyace shi tare da wasu kamfanoni a karshen shekarar 2020 domin neman sake gina tsohon otal din Daula a karkashin Kamfanin Public Private Partnership (PPP).

Sanarwar da Hukumar Kula da Kaddarorin ta fitar kuma ta sanya hannu ta ce, ”Mun gabatar da tayin abubuwa uku da suka hada da Residential – don hada da gidaje 25 na alatu, Cibiyar Kasuwanci, Girman wurare daban-daban na sararin kasuwanci da kuma Daula Boutique Hotel – Rukunim mai daki 90.

“Darajar filin da gwamnatin jihar Kano ta bayar wajen gudanar da aikin tare da ribar da gwamnatin jihar ta amince da ita duk a kudi biliyan biyu da miliyan dari biyu da casa’in da bakwai da dubu sha shida da shida. Naira dari da ashirin da biyu Kobo Tamanin da Tamanin (N2,297,016,622.89) kawai aka mayar da shi Otal.

“A ranar 27 ga Mayu, 2023, tsohon gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya gudanar da bikin kaddamar da otal din kuma an mika shi ga gwamnatin jihar a matsayin kasonta a aikin.

Sai dai mai kula da kadarorin ya ce, “Abin mamaki ne, mun samu kira da misalin karfe 2 na safe ranar Lahadi 4 ga watan Yuni, 2023 cewa jami’an gwamnatin jihar karkashin jagorancin sabon gwamna Abba Kabir Yusuf suka yi i tattaki zuwa wurin da za a yi aikin tare da buldoza, sun ruguje dukkan gine-ginen da ke cikin kasa da suka hada da otal din Daula Boutique mai daki 5 da kuma shaguna 90, da aiki kashi 90% da aka kammala da kuma gidajen zama.

“Mun umurci lauyoyin mu dasu bullo da wani mataki na shari’a akan gwamnatin jihar don neman biyan diyya har naira biliyan 10 da aka riga aka kashe a aikin tare da hana gwamnatin jihar ci gaba da daukar matakan da za su yi mana illa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *