
Alfijr ta rawaito Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya sanar da soke sayar da Asibitin Yara na Hasiya Bayero.
Ana zargin an sayar da asibitin ne a lokacin gwamnatin tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ga wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Gwamna Yusuf ya bayyana haka ne a ziyarar da ya kai asibitin, inda ya jaddada kudirinsa na inganta harkokin kiwon lafiya musamman mata da kananan yara.

A ziyarar tasa, Gwamna Yusuf ya bayyana damuwarsa game da jin dadin jama’a, inda ya jaddada mahimmancin samar da lafiya mai inganci.
Ya kara da cewar, “Lafiyar ‘yan jiharmu musamman mata da kananan yara, na da matukar muhimmanci ga gwamnatina.
Mun kuduri aniyar samar da ababen more rayuwa da ayyuka don tabbatar da jin dadin su.
“Soke sayar da asibitin yara na Hasiya Bayero wani muhimmin mataki ne na cimma burinmu na kiwon lafiya.”
Gwamnan ya kuma tabbatarwa da jama’a cewa gwamnatinsa za ta ba da fifiko kan harkokin kiwon lafiya, inda ya yi alkawarin bayar da jari wajen inganta cibiyoyin kiwon lafiya a fadin jihar.
Ya ce, “Ba za mu yi kasa a gwiwa ba a kokarinmu na bunkasa da inganta kayayyakin kiwon lafiya.
Manufarmu ita ce samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya, da baiwa kowane dan kasa damar samun kulawar da yake bukata.
Gwamna Yusuf ya jaddada muhimmancin tabbatar da gaskiya da rikon amana, inda ya ce, “Za mu gudanar da cikakken nazari don tabbatar da cewa ba a sake samun aukuwar hakan ba.
Yana da matukar muhimmanci a kiyaye kadarorin jama’a da kuma amfani da su domin amfanin jama’a.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
Masha Allah!