Gwamnan Kano Ya Sake Rusa Wasu Manya Manyan Gine-Gine A Daren Asabar

Alfijr ta rawaito Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf a daren ranar Asabar ya rusa wasu gine-gine a Otal din Daula da kuma sansanin Hajji da ke cikin birnin.

A ranar Asabar din da ta gabata ne Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da rusa gine-ginen da gwamnatin ta yi imanin cewa haramun ne a jihar.

Wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Malam Sanusi Bature Dwakin Tofa ya fitar, ta ce rugujewar da aka fara da ginin bene mai hawa uku mai shaguna 90 a kan titin Race Course, a unguwar GRA a Nasarawa, da sanyin safiyar Asabar.

Idan dai za a iya tunawa tsohuwar gwamnatin Dr. Abdullahi Ganduje ta ce gine-ginen da aka gina a Otal din Daula na hadin gwiwar jama’a ne masu zaman kansu.

Yayin da gwamnan jihar ya umurci maginin da ke kula da gine-ginen a sansanin Hajji da ya dakatar da aiki ranar Juma’a a lokacin da ya ziyarci sansanin Hajji.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *