Allah Ya Yiwa Wani Alkalin Babbar Kotun Jiha Rasuwa


Allah Ya yi wa Mai Shari’a Sikiru Adeyinka Oyinloye na Babbar Kotun Jihar Kwara rasuwa.

Marigayin ya rasu ne a ranar Asabar bayan fama da jinya, ya rasu yana dan shekaru 58 a duniya.

A ranar Litinin ake sa ran gudanar da jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tsara a mahaifarsa da ke Jihar Kwara.

A lokacin rayuwarsa, Mai Shari’a Sikiru Adeyinka Oyinloye, ya kasance alkali da ke nuna ba sani, ba sabo.

Ya yanke wa masu damfara ta intanet da dama hukunci tare da kwace kadarorinsu da suka hada da katafarun gidaje da motocin alfarma da kuma dubban daloli, ya damka wa gwamnati.

A shekara 2017 ya sanya tarar Naira biliyan hudu a kan kamfanin jaridar intanet ta Sahara Reporters da mai kamfanin, Omoyele Sowore, kan laifin wallafa labaran karya game da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki a 2015.

Ko da yake daga baya kamfanin ya daukaka kara.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *