Mutane 5 Sun Mutu A Wani Hatsarin kwale-kwale A Jihar Kano


Alfijr ta rawaito akalla mutum biyar ne suka mutu sakamakon hatsarin kwale-kwale da ya rutsa da su a Jihar Kano.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da cewa, wasu matasa takwas ne suka je kogin Panshekara inda suka hau kwale-kwale, biyar daga ciki suka mutu.

“A ranar 21 ga wata, misalin karfe bakwai da minti arba’in da biyar, wasu matasa su takwas da ‘yan unguwar Fagge da Dala suka je kogi na Panshekara inda suka hau kwale-kale.

“A yunkurin tsallaka wannan kogi, kwale-kwale ya kife da mutane bakwai a ciki wadanda suka fada cikin ruwa,” in ji Kiyawa.

Ya kara da cewa an yi yunkuri an ceto mutane guda biyu, sai kuma biyar aka ga gawarwakinsu.

Ya ce an kai su asibitin Murtala da ke birnin Kano, inda a nan likita ya tabbatar da mutuwar tasu.

Yanzu haka ana gudanar da bincike a kan wannan lamarin. In Ji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

One Reply to “Mutane 5 Sun Mutu A Wani Hatsarin kwale-kwale A Jihar Kano”

  1. A tawa fahimtar wannan ai ba maganar da ta shafi Dan sanda bace domin kowa da hakkinsa wannan lamarin ai na fire service ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *