Sakon Sallah Da Bankawa Da Al’ummar Nijeriya – Shugaba Buhari

Alfijr ta rawaito Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya ce sakamakon zaben 2023 ya yi daidai da alkawarin da ya yi na barin gadon zabe na gaskiya da adalci a kasar.

Shugaban ya bayyana haka ne a cikin sakon fatan alheri ga al’ummar Musulmi a kan bikin Eid-el-fitr na karshen azumin watan Ramadan na kwanaki 30.

Sanarwar ta fito ne ta bakin mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, a Abuja ranar Alhamis.

A cewar shugaban, sakamakon zaben 2023 cikin lumana na matsayin daya daga cikin manyan nasarorin da gwamnatinsa ta samu “ban da dan sakaci da aka sami wajen gudanar da zaben a wasu guraren.

Buhari ya bayyana cewa “sakamakon zaben ya yi daidai da alkawarin da na dauka na barin gadon zabe na gaskiya da adalci.

“Ina alfahari da cewa na samar da tsari mai kyau ga duk masu takara ba tare da la’akari da jam’iyya ba don samar da kyakkyawan sakamako ga kowa.”

“Zabe na gaskiya da adalci shine kawai ka’idojin da ke ba da gaskiya ga dimokuradiyyar mu, saboda tauye ra’ayin jama’a yana lalata dimokuradiyya kanta.”

Shugaban ya yi amanna cewa zaben ya kasance a bayyane ta yadda hatta ’yan jam’iyyarsa aka fatattake su, aka yi watsi da su.

Ya kara da cewa “Ko kadan ban tsoma baki a harkar ba domin in baiwa kowa damar da ta dace.”

A cikin azumin watan Ramadan, Buhari ya taya al’ummar musulmi murnar kammala aikin ibada da aka yi.

Yayin da yake addu’ar Allah ya sakawa ‘yan uwa musulmi da suka sadaukar da rayuwarsu a lokutan azumi, shugaba Buhari ya ba da shawarar cewa: “Kada mu manta da muhimman darussa na watan Ramadan, wadanda suka hada da kyautata alaka tsakanin mu da marasa galihu da talakawa.

“Rashin cin abinci da abin sha a lokacin azumi ya sa mu fahimci halin da masu tafiya ba tare da cin abinci ba a kowace rana tare da talakawa. “

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *