Ibtila’i: Gobara Ta Ƙone Wani Gidan Rediyo

Alfijr ta rawaito Gobara ta kone gidan rediyon jihar Oyo (BCOS), a Ibadan babban birnin jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta tashi ne daga dakin studio inda ta yi barna sosai da kayan aiki.

Wani ganau ya ce an gayyaci hukumar kashe gobara ta jihar kuma ana ci gaba da kokarin shawo kan lamarin.

“Gaskiya ne. BCOS yana kan ci da wuta, Ba zan iya ba ku cikakken bayani ba har sai mun sami cikakken bayanin yadda gobarar ta tashi,” inji majiyar.

Hukumar ta BCOS mallakin gwamnatin jihar Oyo ce kuma tana dauke da aikin ilmantarwa, fadakarwa, nishadantarwa da yada bayanai ga mazauna jihar da sauran su.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *