Gwamnatin Najeriya Ta Biya China Da IMF Tare bankin Islama Basussuka Naira Triliyan 3.63

Alfijr ta rawaito Gwamnatin Najeriya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi ta yi nasarar biyan bashin Naira Tiriliyan 3.63 da ke bin asusun lamuni na duniya IMF, gwamnatin China da sauransu.

Hakan ya fito ne daga ofishin kula da basussuka (DMO) a ranar 10 ga Afrilu, 2023.

Bayanai sun nuna cewa Najeriya ta kashe Naira tiriliyan 3.63 wajen biyan basukan ta na waje da na cikin gida a shekarar 2022.

An biya kudaden ga masu lamuni, wadanda suka hada da gwamnatin kasar Sin, bankin Musulunci, bankin Larabawa, asusun ba da lamuni na duniya IMF da dai sauransu.

Bayanai sun kuma nuna cewa Najeriya ta yi amfani da kudin canji na N448.08 wajen biyan basussukan waje na dala biliyan 2.40, wanda ya kai Naira tiriliyan 1.07.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *