Alfijr ta rawaito hukumomi a Jihar Binuwai da ke Nijeriya sun ce akalla mutum 50 sun mutu sakamakon hare-haren da ‘yan bindiga suka kai wani kauye na jihar.

Shugaban karamar hukumar Otukpo Ruben Bako, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AP ranar Alhamis cewa, an kai harin ne ranar Laraba a kauyen Umogidi inda aka kashe mutum 47.
Ya kara da cewa, an yi wa mutum uku yankan rago a kauyen ranar Talata.
Kakakin ‘yan sandan Binuwai Anene Sewuese ya tabbatar da kai harin yana mai cewa maharan sun bude wuta ne a wata kasuwar kauye.
Sai dai Sewuese ya ce mutum takwas ne suka mutu, ciki har da wani dan sanda.
Har yanzu ba a san dalilin kai harin ba, ko da yake hukumomi sun ce hare-haren biyu suna da alaka da juna.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ