
Alfijr ta rawaito tun a watan Yulin 2014 ne gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta nada ta amma an kore ta a shekarar 2015.
A ranar 5 ga Yuli, 2022, shugaba Buhari Ya sake nada ta wa’adin shekaru biyar.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori babbar sakatariyar hukumar bunkasa zuba jari ta Najeriya (NIPC) Saratu Umar.
Matakin ya fara aiki nan take, in ji mai taimaka wa shugaban kasa Femi Adesina a wata gajeriyar sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
Adesina ya kara da cewa, “A cikin umarnin mai girma ministan masana’antu, kasuwanci, da zuba jari, Otunba Richard Adeniyi Adebayo CON, shugaban kasar ya kuma umurci babban darakta a hukumar da ya gaggauta karbar ragamar aiki a cikin riko.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ