Ƴan Sanda Sun Kama Mutum 2 Kan Zargin Kashe Wata Da Ciki A Kano

Alfijr ta rawaito Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta tabbatar da gano gawar wata matashiya ƴar shekara 20 ɗauke da juna biyu kwance a gefen titi a ƙauyen Anadariya da ke ƙaramar hukumar Bebeji.

kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da hakan, ya ce an kama mutum biyu da ake zargi da aika-aikar.

Ya bayyana kamen ne sakamakon rahoton da mazauna yankin suka shigar lamarin da ya sa kwamishinan ƴan sandan jihar, Mamman Dauda ya tura jami’ansa zuwa inda lamarin ya faru.

Kiyawa ya bayyana sunan matashiyar da Theresa Yakubu inda ya ce mutanen da ake zargi da kashe ta saurayinta ne da kuma abokinsa.

A binciken farko saurayin marigayiyar ya amsa aikata laifin inda ya ce cikin da take dauke da shi na sane, kuma ya hada baki da abokinsa su kashe ta bayan da duk wani yunƙuri na zubar da cikin ya gagara.

A nasa ɓangaren, kwamishinan ƴan sandan ya miƙa ta’aziyya ga iyalan marigayiyar inda kuma ya bai wa al’ummar yankin tabbacin cewa za su yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da adalci.

Ya kuma nemi mazauna unguwar su taimaka da bayanan da za su kai ga cafke sauran mutanen da ke da hannu a lamarin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *