Ɗalibi ya kashe ɗalibi ɗan uwansa saboda budurwa a Jami’ar FUDMA Katsina

Screenshot 20231001 114959 com.facebook.katana edit 47698515404700

Abokan takararsa sun yi masa dukan kawo wuka saboda a dakin kwanan dalibai

Alfijir Labarai ta rawaito an kashe wani dalibi saboda bambancin addininsa da na budurwarsa wani rikicin soyayya a Jami’ar Tarayya ta Dutsinma da ke Jihar Katsina.

Ana zargin wasu dalibai ne suka yi wa wani dalibi Abubakar Nasir Barda, da ke aji biyu a jami’ar, dukan kawo wuka da sanduna har ya ce ga garinku nan, a kokarin na raba shi da wata budurwarsa Kirista.

Aminiya ta gano wani dalibi Kirista a jami’ar da ke son budurwar ne da abokansa suka yi wa Abubakar kisan ta hanyar dukan kawo wuka a dakin kwanan dalibai, bayan faruwar lamarin an kwashe shi zuwa asibitin da ke cikin jami’ar, inda rai ya yi halinsa.

Wakilinmu ya samu labari cewa bambancin addini ya yi tasiri a wajen rikici, domin kuwa, wadanda ake zargi da kisan sun yi iya kokarinsu na raba soyayyar ita Alloysious da Abubakar kasancewar addinin su ba daya ba, amma ta ki sauraren su.

Kwafin sanarwar da Muqaddashin Daraktan Tsaron makarantar, Abdulkarim Yahaya ya aike wa shugaban jami’ar a ranar 29 ga watan Satumba, 2023 ta ce dalibar da ake rikici a kanta da wasu dalibai maza biyar da ake zargi suna tsare a hannun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina.

Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Aliyu Abubakar Sadiq ya shaida wa wakilinmu cewa rundunar na bincikar duk wadanda ake zargin kuma akwai alamun bambancin addini ya yi tasiri a cikin lamarin.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Aliyu Abubakar Musa ya yi kira da jama’a su kwantar da hankalin su kuma a ci gaba da bin doka da oda.

Ya kuma roki duk wani mai wani bayani a kan lamarin da ya yi kokarin sanar da hukuma kuma za a ba shi kariya ta hanyar boye sunansa da sauran makamantan haka.

Maihaifin marigayi Abubakar, Malam Nasiru Ibrahim Barda, ya nemi da a bi masa hakkin dansa tare da hukunta duk wani mai hannu a wajen kashe shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

One Reply to “Ɗalibi ya kashe ɗalibi ɗan uwansa saboda budurwa a Jami’ar FUDMA Katsina”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *