Ƴan Ta’adda Sun Kashe Mai Unguwa Sun Yi Awon Gaba Da Wasu A Jihar Kaduna

Alfijr ta rawaito wani mazaunin garin Kaduna Malam Uban Marayu, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun mamaye al’ummar ne a daren Lahadi, inda suka tafi da wasu mutanen da har yanzu ba a tantance adadinsu ba tare da Kadarorinsu.

Wasu ‘yan ta’adda da ake yi wa lakabi da ‘yan bindiga a yankin sun kashe wani shugaban al’umma tare da yin garkuwa da wasu mazauna yankin a wani sabon hari da suka kai a unguwar Liman da ke karamar hukumar Birnin-Gwari a jihar Kaduna.

An tattaro cewa ‘yan ta’addan sun kuma yi barazanar sake kai hari ga al’umma, kamar yadda The PUNCH ta ruwaito.

“Sun zo jiya (Lahadi) da misalin karfe 10:00 na dare.

Sun kai hari a gefen Birnin-Gwari inda suka kashe Mai Unguwa a Unguwan Liman mai tazarar kilomita 3 daga garin Birnin-Gwari. in ji shi.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, babu wani martani a hukumance daga gwamnatin jihar ko kuma ‘yan sanda, duk da kira da sakon karta kwana da aka yi wa jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Muhammad Jalige.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *