Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Kan Jami’an ofishin Jakadancin Amurka Mutane 4 Sun Mutu

Alfijr ta rawaito an harbe wasu ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka hudu a Najeriya da ke aikin jin kai a jihar Anambra bayan wani hari da aka kai musu a ranar Talata.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata a yankin Amiyi/Eke Ochuche da ke karamar hukumar Ogbaru ta jihar.

Kawo yanzu dai ba a gano wani dalili ba, sai dai wata majiya a yankin ta ce maharan sun yi musu kwanton bauna kuma nan take suka bindige wadanda aka kashe din.

Sai dai wata majiya ta ce maharan sun haifar da firgici a yankin yayin da suka mamaye filin inda wasu daga cikin mazauna unguwar suka taru suna jiran jinya daga jami’an UNICEF.

Majiyar ta ci gaba da cewa, “An yi musu kwanton bauna ne, an kuma harbe kusan hudu daga cikinsu, yayin da wasu kuma suka samu raunuka daban-daban yayin da suka tsere da motarsu mai dauke da rubutu, UNICEF.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *