Ƴan sanda Sun Damke Ƴan Daba 61 Kan Zargin Ta’adda Da Ƙwace Wayoyi Yayin Taron Tinubu


Alfijr ta rawaito Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta yi holin wasu matasa su 61 da ta cafke bisa zargin su da ayyukan ta’addanci ta hanyar ƙwacen wayoyin mutane a ranar Larabar yayin taron kamfe na Bola Tinubu ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.

Rundunar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ta SP Abdullahi Haruna, ya fitar a daren Alhamis ɗin da ta gabata ga manema labarai.

Sanarwar ta ce, an cafke matasan ne ɗauke da makamai da miyagun ƙwayoyi yayin gudanarda taron a filin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata.

Kiyawa ya ce, an samu matasan da makamai da suka haɗa da wuƙaƙe guda 33 da adda 8 da almakashi guda 4 sai da tabar Wiwi sinƙi daya da sauran kayayyakin maye.

Ya Kara da cewa, Kwamishina ƴan sandan Kano Mamman Dauda ya bayar da umarnin gurfanarda matasan da ake zargi a gaban Kotun Majistri dake Normans land domin girbar abinda suka shuka.

 Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Best seller Channel
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *