Ƴan Bindiga Sun Sake Garkuwa Da Fasinjoji A Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

Alfijr ta rawaito wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji guda 3 a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi tsakanin garin Dikko da Jere bayan da motar da ke dauke da su ta lalace suka tsaya domin dubawa.

Daya daga cikin wadanda harin ya rutsa da su mai suna Sadiya Ahmed da abokan tafiyarta an ce sun dauki hayar motar da niyyar yin balaguro zuwa Abuja.

Wata majiya mai tushe da ta yi magana da jaridar DAILY NIGERIAN a ranar Litinin, ta ce barayin sun tuntube iyalan wadanda abin ya rutsa da su, inda suka bukaci a biya su Naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *