Ƙarancin Rumfunan A Mina Ya Janyo Dubban Alhazan Najeriya Fadawa Ƙaƙanikayi

Dubban Alhazan Najeriya ne suka fake a wajen rumfunar Alhazai a Mina saboda karancin su.

Alfijir Labarai ta rawaito wakilin jaridar Premium Times Hausa da ya ke wannan wuri ya bayyana cewa da yawa daga cikin mahajjatan sun maƙale ne a jikin rumfunar dalilin karancin rumfunar.

Baya ga tsananin zafin rana da ake yi, ga kuma rashin wurin zama, mahajjatan Najeriya a Mina na fama da ƙarancin abincin ci.

Wani mahajjaci daga jihar Oyo da wani daga Katsina sun ce ” Gaba ɗaya yau bamu saka komai a cikin mu ba, kuma babu abincin da zamu ci ma saboda mahukunta ba su kawo ba sannan babu inda za ka siya ka ci.

Ya kuma lura cewa rumfunar da aka ware wa dubban ƴan Najeriya ab zai ishe su ba, karshen ta dai dubbai za su rika kwana ne a waje sannan kuma ga ƙarancin abinci da suke fama da shi.

Shugaban hukumar Alhazai na kasa, Zikirullah Hassan ya bayyana cewa matsala ce aka samu daga mahukuntan kasar Saudiyya.

” Mun biya dukka kudaden da suka bukata, kuma sun bayyana mana cewa suna da makeken ɗakin dafa abinci da zai wadatar da duka Alhazan mu. Amma kuma sai muka ga ba haka ba.

Zikirullah ya ce sun tattauna da jami’an Saudiyya kuma za su ci gaba da tattaunawa domin a samu mafita cikin gaggawa.

Sai yanzu haka Auwal Ibrahim Hussain ya tabbatarwa da Jaridar Alfijir Labarai cewar yanzu haka abinci ya wadata a ko ina a filin Minna sabanin dazu kamar yadda aka yi karancin abinci.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

One Reply to “Ƙarancin Rumfunan A Mina Ya Janyo Dubban Alhazan Najeriya Fadawa Ƙaƙanikayi”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *