Rundunar ƴansanda ta jihar Kano ta ce ta kama ɓarayin mota guda sha biyar a jihar.
Alfijir labarai ta rawaito wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a Kano, ya ce rundunar ta kuma samu nasarar ƙwato ababen hawa guda 20.
Ya ce rundunar ta samu wannan nasara ne sakamakon jajircewa wajen yaki da aikata laifukan a jihar.
Ya ce rundunar na wannan jajircewa ne daidai da umarnin Babban Sufeto-Janar na Ƴansanda, Egbetokun, na kokarin yakar aikata laifuka a cikin al’ummma.
Kiyawa ya kara da cewa Kwamishinan Ƴansandan jihar, CP Usaini Gumel ya godewa al’ummar jihar bisa hadin kai da su ke baiwa rundunar wajen kokarin ta ndnsamar da zaman lafiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp