Ƴan Sanda Sun Cafke Matasa 3 da Zargin Yi Wa ‘Yar Shekara 15 Fyade

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama wasu matasa uku da ake zargi da yi wa wata yarinya ‘yar shekara 15 fyade a jihar Adamawa.

Alfijir Labarai ta rawaito wadanda aka kama bisa zargin yi wa karamar yarinya fyade sun hada da Hassan Nasir, Uzairu Danfulani da kuma Yahya Edward.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ya shaida wa manema labarai a safiyar Laraba cewa wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a karamar hukumar Mayo-Belwa da ke jihar.

Ya ce, “Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa a ranar 20/07/2023 ta kama wasu mutane uku (3) da ake zargi da laifin yi wa karamar yarinya ‘yar shekara 15 fyade a karamar hukumar Mayo Belwa.

“Wadanda ake zargin sun hada da: Hassan Nasir, dan shekara 25, mazaunin Sabon Pegi Ngurore, karamar hukumar Yola ta Kudu, Uzairu Dan Fulani, mai shekaru 25, mazaunin Gasabga ward Mayo belwa, karamar hukumar Mayola Belwa da Yahaya Edward mai shekaru 26, mazaunin Sabon Pegi, Ngurore, karamar hukumar Yola ta kudu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *