Ƴan Sanda sun cafke mai ƙerawa ƴan ta’adda makamai a Jigawa

Screenshot 20220927 114744 com.facebook.katana edit 3794567887961

Rundunar ƴansanda a Jihar Jigawa ta samu nasarar kama wani mutum dan shekara 50, da take zargi da kera makamai a Karamar Hukumar Ringim.

Alfijir Labarai ta rawaito Kakakin rundunar a jihar, mukaddashin sifuritendan ‘yan sanda Lawan Shisu ne ya tabbatar da hakan ranar Alhamis.

A cewar Shisu, sun kama mutumin ne a ranar 16 ga watan da muke ciki.

“Rundunar ’yan sanda da hadin gwiwar ’yan sa-kai sun kama wanda muke zargi da kera wa bata-gari makamai a garin Yandutsen Kawari,” inji Kakakin ’yan sandan.

A binciken da aka gudanar a gidansa, an samu kananan bindigu biyu kirar gida, da kuma wasu manya biyu.

Shisu ya ce wanda suke zargin, da kansa ya tabbatar musu cewa yana kera makamai da dama, kuma sau tari bai san wadanda yake sayarwa ba.

Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇

https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI

SP Lawan Shisu ya ce da zarar sun kammala bincike za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *