Ƴan Sandan Jihar Kano Sun Cafke Shugaban Jam’iyyar APC Da Sama Da Katin Zabe PVC 300

Alfijr ta rawaito jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) da kungiyoyin farar hula a karkashin inuwar jam’iyyar adawa ta APC sun bukaci da a gaggauta gurfanar da shugaban jam’iyyar APC da aka kama yana rike da sama da katiin mutum dari uku (300) na dindindin na Zaɓe PVC a Kano.

Alfijr Labarai

Wanda ake zargin dai an kama shi ne da Aminu Ali Shana wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC na gundumar Yautan Arewa, karamar hukumar Gabasawa ta jihar Kano a ranar Juma’a 14 ga watan Oktoba, 2022.

Laifin ya sabawa sashe na 21 da 22 karamin sashe na 1 (a), (b) ) da (c) na dokar zabe ta 2022 kamar yadda aka yi wa kwaskwarima.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan ta mika wanda ake zargin zuwa sashen binciken manyan laifuka (CID) na jihar Kano da ke Bompai domin ci gaba da bincike.

Alfijr Labarai

A wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Kano, shugaban NNPP na jihar Kano Hon. Umar Haruna Doguwa ya umurci kungiyar lauyoyin jam’iyyar da ta shigar da kara a kan wanda ake zargin da kuma masu daukar nauyinsa.

“Na umurci mai ba mu shawara kan harkokin shari’a da ya rubuta wa alkalan zabe (INEC) domin a bibiyar matakin da ya dace a kan lamarin.”

Doguwa ya tabbatar a cikin sanarwar. gabanin babban zaben 2023.

“A bisa ka’ida an tabbatar mana da wannan kamun, muna ci gaba da nuna yatsa yayin da muke jiran mataki na gaba da hukumar zabe mai zaman kanta da ‘yan sandan Najeriya za su dauka.”

Alfijr Labarai

NNPP ta ce za ta ci gaba da bin wannan shari’ar zuwa ga cimma matsaya don kare martabarta,
ka’idojin dimokuradiyya.

A wata sanarwa da Abdullahi Ibrahim Rogo ya raba wa manema labarai sakataren yada labaran NNPP na jihar ya ce shugaban jam’iyyar ya yaba da kokarin rundunar ‘yan sandan jihar Kano tayi na tabbatar da gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin da zai kai ga ci gaba da kama wasu da ake zargi.

Hon. Doguwa ya kuma yi nuni da cewa, yunkurin da jam’iyyar APC mai mulki ta yi na rage yawan kuri’u a zabukan 2023 mai zuwa, domin tauye damar jam’iyyar NNPP a Kano da Najeriya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Nigerian Tracker

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *