Hakan na zuwa ne lokacin da matar ta ga yaron a dakinsa tare da budurwarsa
Alfijir Labarai ta rawaito wata uwar mai suna, Maryam Zakari, an yi zargin cewa ta yiwa ɗan ta Abdulahi wanka da ruwan zafi, saboda ya yi yunkurin kawo budurwarsa gida a jihar Kuros Riba.
An ce matar ta tafasa ruwan sannan ta shekawa dan nata a ranar Alhamis din da ta gabata, wanda hakan ya sa ya samu munanan raunuka.
Lamarin ya faru ne a Bogobiri, unguwar Hausa-Fulani a cikin birnin.
Hakan na zuwa ne lokacin da matar ta ga yaron a dakinsa tare da budurwarsa maimakon ta gargade shi da baki, sai ta yanke shawarar shwka masa ruwan zafi.
Ta zuba masa ruwan zafin a jikinsa ta kuma yi ihu tana neman agaji,” inji Dauda.
A lokacin da jaridar Vanguard ta ziyarci gidan da abin ya faru, an ga jama’a da dama sun je domin kallewa idon su, inda da dama suka yi ta caccakar matar kan matakin da ta dauka.
“Ba batun budurwar ne kawai ba, akwai jargin dan baya bata kulawar da ta dace ta yau da kullum, sai dai ya kashewa budurwar sa kudade,” in ji Dauda.
Tuni aka garzaya da shi zuwa wani asibiti mai zaman kansa a Calabar domin kula da lafiyarsa.
Da aka tuntubi jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Irene Ugbo, ta ce har yanzu ba a kai mata rahoton lamarin ba.
Kokarin yin magana da Mahaifin yaron da wadda tayi abin wato mahaifarsa ya ci tura.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@musa_bestseller
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM