Kungiyar masu sarrafa shinkafa ta Nigeria, wato RIMAN, ta bayyana damuwa game da matakin gwamnatin kasar na dage haramcin shigar da wasu kayayyaki daga kasashen waje ciki har da shinkafa.
Alfijir Labarai ta rawaito Shinkafa na cikin kayayyakin da gwamnatin Najeriya ta haramta shigar da su a shekarar 2015 cikin kasar a wani mataki na kokarin bunkasa noma a kasar da nufin dogaro da kai.
Kungiyar masu sarrafa shinkafar ta cikin gida, ta ce matakin dage haramcin babbar barazana ce bayan sun zuba makudan kudi a kasuwancin.
Shugaban kungiyar, Peter Dama, ya shaida wa BBC cewa, a gaskiya wannan mataki ya zame musu kamar bala’i ne domin gwamnati ta sanya sun sanya kudadensu sun sayi kayan sarrafa shinkafa, sannan an sa jama’a sun shiga noma shinkafar, ga shi jama’ar kasa sun fara son shinkafar da ake samarwa a gida, “sai kawai mu ji an ce an dage haramcin shigo da shinkafar waje.”
Ya ce, “ Wannan mataki na gwamnati ya kawo mana cikas, ga shi kuma zai sa a rufe kamfanoni da dama, sannan jama’a da yawa za su rasa aikin yi ga shi kuma manoma da dama kuma ba za su yi aikin shinkafa, kuma sannan za a fara shigo mana da shinkafar da ta riga ta rube.”
Peter Dama, ya ce: ‘’Gwamnati ba ta shawarce mu ba kafin ta dauki wannan mataki, kuma batun cewa shinkafar da ake samarwa a gida ma tana tsada ai kowa ya san ba da ruwa ake nomata ba, kuma yadda ake noman nata ma ai sai a duba a gani, sannan wajen ban ruwa ba wasu da kananan inji suke yi kuma ai da man fetur ake amfani a injin, kuma kowa ya san tsadar mai a yanzu.”
Shugaban ya ce babbar damuwarsu idan har aka fara shigar da shinkafar waje to mutane sai su koma kanta domin su al’ummar Najeriya idan aka ce musu ga wani abu na waje ko da ruwan sha ne sai hankalinsu ya koma kansa.
Ya ce, “ Mu mun yi iya bakin kokarin mu wajen nunawa ‚yan Najeriya cewa shinkafarmu ta gida ta fi afki sannan ta fi amfani a jiki domin mu ta mu ba a ajiye ta ta yi shekara da shekaru ba.”
“ Mu ba ma yi wa shinkafarmu ta gida doguwar ajiya.”
Ya ce, “A yanzu mu matakin da za mu dauka shi ne za mu yi magana da gwamnati mu ba ta shawara, sannan mu saurara mu ji ko za su saurari kokenmu.”
Peter Dama, ya ce,” Idan har ana so a samu saukin tsadar shinkafa a kasa to sai a rage kudin man fetur da na kayan aikin gona, da kuma ba wa manoma taimakon da zai bunkasa nomansu.”
BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo
Wlh WANAN ABINDA GWAMNATI SHINE DAIDAI,SABODA RIFE BODAR DA TAYI YASA MANOMA DA YAN KASUWA SUN TAKURAWA TALAKA,SABODA MA’AIKATA BASA CIKIN WALWALA,KUNIN FARASHI HAUHAWA YAKE ALBASHI KUMA BA KARUWA YAKE BA,KAI SHUGABAN KAMFANI MAI YASA TUNDA TALAKA YAKE CIKIN KUNCI BAKA FITO KAYIWA TALAKA BAYANIN RIBAR DA KUKA SAMU TA SAMA DA SHEKARU 8 BA,SAI YANZU DA TALAKA ALLAH YA KARBI ADDU’AR SA,ZAKA FITO KA GAYA MASA FADUWA,WLH ALLAH YA TABBATAR MANA DA HAKAN YA ZAMEWA TALAKA SAUSAUCI NA SAMUN ABINDA ZAICI A FARASHI MAI SAUKI,KU KUMA ALLAH YA MASANYA MUKU DA MAFI ALKHAIRI ALLAHUMMA AMEEEEN
Da da ba’a cire tallafin mai din ma baku sausauta ba,a shekara 8 yan kasuwa da manoma ke Jin dadi a Nigeria,mai yasa Baku jeba Kun ma GWAMNATI SHAWARA BA
Wadan nan manoma da ‘yan kasuwa da suke sukar wannan shirin gwamnati na bude boda, wlkh ba kananan mjgaye ba ne!
Mu a kullum, arzikin kasarmu ke ta gasa mana aya a hannu!!
Fetur namu ne, amma ya fi karfin talaka.
Abinci noman mu ne amma ya fi karfin talaka.