Ƴan Sanda Sun Damƙe Ƴar TikTok Ɗin Nan Murja Kunya A Kano

Alfijr ta rawaito Jami’an ƴan sanda sun kama fitacciyar jarumar wasan barkwanci a TikTok, Murja Kunya a otal din Tahir da ke Kano.

Ƴan sandan sun kama ta ne a lokacin da ta ke kokarin kama wa baƙin ta na kusa da na nesa da za su zo bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta da aka yi ta yadawa.

Ko a watan Satumban shekarar da ta gabata, wata kotun shari’ar Musulunci ta rubuta wa kwamishinan Ƴan sandan jihar Kano wasika da ya kama da bincikar Kunya tare da wasu ƴan TikTok bisa zargin lalata tarbiyyar matasa.

Sauran ƴan TikTok da ke cikin wasikar sun hada da Mr 442, Safara’u, Dan Maraya, Amude Booth, Kawu Dan Sarki, Ado Gwanja, Ummi Shakira, Samha Inuwa da Babiana.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *