
Alfijr ta rawaito Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta yanke shawarar shiga yajin aikin sai baba ta gani a ranar laraba 7 ga watan yuni mai kamawa.
Ta Ayyana yajin aikin ne saboda janye tallafin mai da gwamnati ta yi.
Shugaban kungiyar Joe Ajaero shi ne ya sanar da haka, bayan wani taron gaggawa da shugabannin kungiyar suka yi yau Juma’a a Abuja.
Idan zaku tuna tun a ranar 29 g watan Mayu shugaba Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur, in da sanarwa ta shugaban ta janyo tashin farashin man a sassan kasar, inda aka rinka samun dogayen layukan ababan hawa a gidan mai.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ