Zanga-zanga Ta Barke A Senegal Bayan Sanar Da Dage Zabe

IMG 20240205 061416

Jami’an tsaron kasar Senegal sun tarwatsa cincirindon jama’a da suka taru a Dakar babban birnin kasar a jiya Lahadi domin nuna adawa da dage zaben shugaban kasar da aka yi, wanda a da za a yi shi ne a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Alfijir labarai ta rawaito Shugaba Macky Sall ya sanar a ranar Asabar din da ta gabata cewa za a jinkirta kaɗa kuri’ar zuwa ranar da ba a bayyana ba saboda takaddama kan jerin ‘yan takara – matakin da jam’iyyun adawa suka yi watsi da shi.

Kimanin masu zanga-zanga 200 ne suka hana zirga-zirgar ababen hawa a babbar titin birnin Dakar tare da saka shingayen na ƙonannun tayoyi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

‘An kama tsohuwar Firaimminista’

An kama tsohuwar Firaiministar Senegal Aminata Toure, wadda a yanzu ita ce babbar ‘yar gaba-gaba a zanga-zangar nuna adawa da dage zaben shugaban kasa, kamar yadda dan majalisar jam’iyyar adawa Guy Marius Sagna ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

“Na tabbatar da cewa ‘yan Jandarma sun kama Aminata Toure,” in ji shi. Shugaban kasar Macky Sall ne ya nada Toure firaiminista kafin daga baya ta koma jam’iyyar adawa.

Daruruwan magoya baya na adawa da ke zanga-zangar sun koma kan gefen titunan bayan ‘yan sandan kwantar da tarzoma sun harba hayaki mai sa hawaye. Har yanzu dai hukumomin kasar ba su ce komai ba kan sabon lamarin.

Senegal dai ba ta taba jinkirta zaben shugaban kasa ba kuma akwai rashin tabbas kan abin da zai biyo baya.

ECOWAS ta bukaci a kwantar da hankula

A bara, kasar ta fuskanci mummunar zanga-zanga bayan da aka daure jagoran ‘yan adawa Ousmane Sonko, inda magoya bayansa suka ce wata dabara ce ta hana shi tsayawa takara a zaben.

Shekaru da dama ana kallon Senegal a matsayin daya daga cikin kasashen Yammacin Afirka mafi kwanciyar hankali a tsarin dimokuradiyya, amma ci gaban siyasa a kasar ya haifar da damuwa.

Bayan sanarwar da Sall ya yi ta kafar talabijin, kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ta nuna damuwa game da yanayin da ya kai ga ɗage zaben, tare da yin kira da a sanya sabuwar ranar zabe cikin gaggawa. An kuma bukaci a kwantar da hankula da bin matakin sasantawa.

TRT Afrika

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *