Daga Shu’aibu I. Gusau
Alfijr ta rawaito Gwamnan jihar Zamfara, Hon. Bello Mohammed Matawalle ya bayyana cewa zasu gurfanar da wadanda ake zarginsu da daukar muggan makamai, ciki har da ‘wadanda aka Kama da Bindiga kirar AK- 47, a Gaban Kuliya.
Matawalle ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidansa da ke garin Maradun da ke karamar hukumar Maradun,ya ce wasu wadanda ake zargin ‘Yanbangar siyasar adawa ne, musamman wadanda suka Gudanar da taro a baya-bayan nan,
Ya ce jami’an tsaro ne kawai doka ta ba su damar daukar bindigogi kirar AK-47 ko duk wani nagartaccen makami.
“Ina mamakin abin da fararen hula za su iya yi da bindigogin AK-47 ko wasu muggan makamai idan ba ‘yan ta’adda bane kai,” in ji shi.
A cewarsa, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban wata kotun da ke da hurumin shari’a da zarar an kammala cikakken bincike.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇