Shugaban Kungiyar Zauren Hausa, Farfesa Ibrahim Garba Satatima, ya gabatar da doguwar mukala akan kalubalen da koyon harshen Hausa ke fuskanta a makarantu da kuma hanyoyin da za a magance su.
Haka kuma ya ce manufar shirya taron shine kara habbaka harshen da kuma inganta shi domin a dada dawo da martabar harshen da al’adun Hausawa na asali.
Dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Madobi a majalisar dokokin jihar Kano, Honarabul Sulaiman Mukhtar Madobi, ya buƙaci al’ummar jihar da su hada kai wajen samar da dokar da zata wajabtawa dukkan daliban da ke karatu a jihar koyon yaren Hausa.
Honarabul Madobi, na bayyana hakan ne a yayin taron Kungiyar Zauren Hausa na shekarar 2025, inda ya ce hakan shine abinda ya kamata la’akari da yadda ake kokarin kassara yaren ta hanyoyi da dama.
Haka kuma ya bayyana takaicinsa dangane da yadda mutane suke kyamatar harshen hausa, ta hanyar aro wasu yarikan wadanda ba zasu amfanar da su komai ba, kuma hakan ya cutar da wannan al’umma a tsawon lokaci.
Dan majalisar ya shawarci hausawan duniya da su bawa harshen su fifiko ta hanyar yinsa a harkokin su na yau da kullum tunda shine abinda ya kamata su bawa fifiko fiye da kowanne yare a rayuwar su.
Haka kuma ya ce kofarsa a bude take wajen samun goyon bayan al’ummar Kano domin ya gabatar da kudirin a majalisar dokokin jihar don ya zama doka, ta yadda za a kara bunkasa harshen duba da mafi yawancin manyan kasashen duniya sun fi bawa yaren iyayen su da kakanni fifiko ba wai na Baki ba.
A nata jawabin, Malama a sashen koyar ilimin magungunan gargajiya da al’adun Hausa a Jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Maryam Mansir Yola, ta shawarci al’ummar Hausawa da su kara rike harshen Hausa da kuma al’adunsu la’akari da yadda suke da kyau da asali tun kafin zuwan turawa.
Shima Shugaban Kwalejin share fagen shiga Jami’a ta jihar Kano (KACEPS), Dakta Sunusi Yakubu, ya buƙaci kungiyar ta samar da makon Hausa domin masana su sami damar baje-kolin su akan yaren ta yadda za a kara nunawa yara masu tasowa muhimmancin sa.
Ya kuma kalubalanci kafafen yaɗa labaran jihar Kano da Arewacin Najeriya akan yadda ake saka tallace-tallace da gurbatacciyar Hausa, ko kuma muryar wadanda bama hausawan bane gaba daya, inda ya yi fatan su samar da tsarin da zai magance matsalar.
Sauran wadanda suka baje-kolin su a wajen taron sun hadar da dan majalisar dokokin jihar Kano ne wakiltar Ungogo, Honarabul Aminu Sa’ad Ungogo, Wakiliyar Shugaban Subeb, kuma Darakta kula da harkokin koyo da koyarwa, Hajiya Magajiya Usman, Wakilin Shugaban hukumar tarihi da al’adu na jihar Kano, Malam Kabiru Musa Bichi, da dai sauransu.
Taron ya gudana ne a safiyar asabar Asabar 5 ga watan Yuli 2025, a dakin taro na Farfesa Hafizu Abubakar dake Jami’ar Yusif Maitama Sule ta Kano, inda ya sami halartar masu ruwa da tsaki a fannin ilimin jihar Kano, dumbin dalibai a kanana da manyan makarantun jihar da na makwabtan jihohi.





Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD