Wata Yarinya Ƴar shekara 17 Ta Rataye Kanta Da Kanta A Kano

Alfijr ta rawaito Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce tana ci gaba da bincike kan abin da ya sa wata budurwa mai shekara 17 ta rataye kanta a ƙauyen Garin Dau da ke yankin karmar hukumar Warawa cikin birnin dabo

Yawancin mazauna ƙauyen dai sun yi zargin cewar budurwar ta rataye kan nata ne bisa auren dole da iyayenta ke shirin yi mata.

A nasu bangaren iyayen nata sun musanta wannan zargi inda suka ce ba ta kammala makarantar sakandare ba, balle a yi maganar aura da wani na.

Alfijr
Wannan al amari ya zo wa mazauna yankin da cikakken mamakin, sakamakon yadda yarinyar ke da kyawawan ɗabi’u da sanin girman kowa.

A yau ne aka shiga yini na biyu na rasuwar Safiya mai shekaru 17 da ke aji biyu a makarantar sakandare, wadda aka tarar da gawarta a rataye kuma ana zargin ita ta rataye kanta.

Alfijr

SP Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne mai magana da yawun rudunar ƴan sanda a Kano, ya tabbatar da samin labarin faruwar lamarin, kuma suna bincike kan lamarin don gano shin budurwar ce ta rataye kan nata ko kuwa wani ne.

Kamaru yadda BBC suka wallafa