Alfijr Labarai
Ƙungiyar ‘Yan Jarida Na Fafutuka Don a Hukunta Mutumin da Yayi wa Tsohuwar Matarsa ‘Yar Jarida Dukan Kawo Wuƙa
Alfijr ta rawaito kungiyar ‘Yan Jarida ta NUJ a jihar Adamawa ta shirya tsaf don fafutukar ganin an hukunta Mal Ibrahim Aliyu wanda tsohon ma’akacin hukumar wutan lantarki ta Najeriya ta PHCN, wanda ake zargin yayi wa tsohowar matarsa, Nafisa Vandi dukan kawo wuƙa.
Shugaban ƙungiyar ‘yan jarida ta kasa, reshen jihar Adamawa, Ishaka D. Dedan ya fitar da wata sanarwa da a ranar Laraba kan lamarin
Alfijr Labarai
Ishaka ya shaida cewa Nafisa Vandi ‘yar jarida ce da ke aiki da kafar yaɗa labarai ta ABC , yace tsohon mijinta wanda korarren ma’akacin PHCN ne yayi mata ɗan karen duka wanda yayi sanadiyar ji mata ciwo don haka suke neman a bi mata haƙkinta a hukunta wanda ake zargin.
Sanarwar ta ce duk da dai ‘yan sanda sun kama wanda ake zargin, ƙungiyar na fatan ayi masa hukuncin cikin lokaci inda ta neme sauran ƙungiyoyin kare hakkin mata na duniya da su shiga lamarin don samun ingantaccen adalci