Alfijr
Alfijr ta rawaito rundunar ƴan sandan jihar Bauchi da ke Najeriya ta tabbatar da kai hari tare da sace maigarin ƙauyen Zira mai suna Alhaji Yahya Abubakar da kuma ɗansa wato Habibu Saleh a ƙaramar hukumar Toro.
Mai magana da yawun rundunar SP Ahmad Wakil ne ya fitar da sanarwar ga manema labarai.
Alfijr
SP Wakili ya Kara da cewar yan bindigar sun shiga ƙauyen ne da misalin ƙarfe sha biyu na dare a ranar Lahadi sannan suka sace mutanen
Ya kuma ƙara da cewa, yanzu haka jami’an tsaro sun shiga cikin daji don neman inda aka ɓoye waɗanda aka sace.
Alfijr
Muna kara bai wa al’umma tabbacin cewa za mu kwato waɗanda aka sace, da fatan za a cigaba da bamu hadin kai kamar yadda aka saba. Inji shi