Wata Gobara Ta Tashi A Kasuwar Singa Da Ke Birnin Kano

Alfijr ta rawaito Hukumar kashe gobara ta jihar Kano a ranar Litinin  ta tabbatar da cewa gobara ta kone wasu shaguna da ba a tantance ba da kuma babban ginin tsohon bankin Savannah da ke kasuwar Singer a Kano.

Sanarwar da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi ya fitar ta ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 02:18 na dare.

“Mun samu kiran gaggawa da tsakar dare da misalin karfe 02:18 na dare daga wani Sai’du Hamza cewa gobara ta tashi a kasuwar da ke karamar hukumar Fagge a jihar.

“Da samun labarin, mun yi gaggawar aika wasu jami’an mu da motar kashe gobara zuwa wurin da lamarin ya faru da misalin karfe 02:22 na safe domin kashe gobarar domin kada ta shafi sauran shaguna,” inji shi.

Sai dai Abdullahi ya ce gobarar ta kone shaguna na wucin gadi da dama, ya kara da cewa har yanzu hukumar ba ta gano musabbabin faruwar lamarin da kuma adadin shagunan da lamarin ya shafa ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *