
Alfijr ta rawaito Wasu ‘yan bindiga, da suka kai hari kan al’ummar Maikatako, a karamar hukumar Bokkos ta Jihar Filato, sun kashe mutum tara na dangi daya da wasu da dama.
DSP Alfred Alabo, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ne, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Laraba a Jos.
Hukumar ƴan Sandan jahar ta yi alkawarin bayar da karin bayani kan lamarin, ta ce an tura jami’an rundunar zuwa ga al’umma domin samun kwanciyar hankali. “
Yanzu haka mutanen mu suna bin maharan; muna kan binciken halin da ake ciki, amma har yanzu cikakkun bayanai game da harin basu kammala ba,” inji shi.
Sai dai, wani mazaunin unguwar ya shaida wa NAN cewa kawo yanzu a binciken da ‘yan kungiyar suka yi, an gano gawarwaki 18.
A cewar Mista Ayuba, ana samun tashin hankali sosai a cikin al’umma, har ma da kasancewar ‘yan sanda da sojoji.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ