
Alfijr ta rawaito Wani dan kasar Laberiya mai suna @Realcharley22, dandalin sada zumunta na Tiktok ya dakatar da shi, saboda yada labaran karya kan da diyar mataimakin shugaban Najeriya, Kiki Osinbajo.
Mai yaɗa karyar ya bayyana a TikTok cewa an kama Kiki a Burtaniya saboda tana da makudan kudade a daloli.
Wanda ake zargin ya buga hotuna da bidiyo don tabbatar da wannan ikirarin, sai kuma daga baya ya fito ya karyata labarin, bayan da wani mai wallafa labaran Najeriya, Tunde Ednut, ya wallafa cewa ba gaskiya ba ne.
Sakamakon haka yan Najeriya da yawansu sun garzaya don kai rahoton shafin na yaudarar jama’a tare da duba shafin a ranar Asabar.
@Realcharley22 sa’o’i 24 da raba bidiyon na karya, ya sake yada wani faifan bidiyo yana neman afuwar Kiki da ‘yan Najeriya kan wannan post din yana mai cewa majiyarsa ta rikitar da matar a cikin bidiyon na Kiki.
Ya sake bayyana cewar, “Ina so in nemi gafarar Kiki Osinbajo domin ba a kama ta ba.
Labarin ba gaskiya bane kuma majiyata ta yaudare ni ta dauki wani a matsayin Kiki.
“Ina so in yi tsokaci kan faifan bidiyon da na wallafa a baya, kuyi hakuri, mabiyana da Kiki Osinbajo, ba a kama ta ba.
“Shahararren marubucin nan na Najeriya, Tunde Ednut ya tabbatar a Instagram cewa karya ne, Kiki ba a taba kama ta ba.
Ya ce in sauke labarin kuma an tabbatar da cewa labarin karya ne.”
An bayar da rahoton cewa Kiki ta tashi zuwa Abuja tare da mahaifinta a ranar Talata bayan tafiyar VP zuwa Legas, inda ya yi magana a taron kungiyar yawon bude ido ta Majalisar Dinkin Duniya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ