Shugaba Tinubu Ya Fara Naɗa Mukamin Farko Bayan Rantsar Dashi

Alfijr ta rawaito Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Dele Alake a matsayin mai magana da yawunsa, sa’o’i kaɗan bayan rantsar da shi a yau Litinin.

Alake ya dade tare da Tinubu, in da har ta rike mukamin kwamishinan yada labarai da dabaru a ƙarƙashin Tinubu da ga 1999 zuwa 2007 a lokacin ya na gwamnan jihar Legas.

Haka kuma shugaban ya nada Ambasada Kunle Adeleke a matsayin zagin shugaban ƙasa.

Ya kuma naɗa shugaban matasan APC na kasa, Olusegun Dada a matsayin mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan kafafen yaɗa labarai na zamani.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

One Reply to “Shugaba Tinubu Ya Fara Naɗa Mukamin Farko Bayan Rantsar Dashi”

  1. Na amince da su, amma ba a cikin saka-shakawa ne da ni masu jajirce don samun buƙatar fitar da bayanan da ke dauke da Bola Ahmed Tinubu, a yau Litinin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *